Mutumin mai suna James Meyers ya ce ya na zaune
a cikin motarsa kawai sai ga jami'an tsaro suka ce an
ba su takardar izinin kama shi.
A shekarar 2002 ne dai Mr Meyers ya je wani shagon
bada hayar Kaset na J&J ya ari Kaset din barkwanci,
kuma tuni aka rufe shagon.
An gurfanar da shi gaban kotu, amma tun kafin a fara
shar'ar aka sallame shi, bayan ya biya tarar dala 200.
Mr. Meyers ya ce wannan ne karon farko da aka fara
saka masa ankwa a hannu.
No comments:
Post a Comment